rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa China Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mai zanen gidaje dan asalin China da Amurka Ieoh Ming Pei ya rasu

media
Leoh Ming Pei mai zanen gidaje dan asalin kasar China PAUL HAWTHORNE / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP

Shahararren mai zane gidaje dan asalin kasar China da Amurka Ieoh Ming Pei wanda ya taimaka wajen tsara ginin shahararren gidan ajiye kayayyakin tarihi na Louvre da ke Paris ya rasu yana da shekaru 102.


Gwamnatin Faransa ta nuna alhinin ta tareda bayyana Leoh Ming Pei a matsayin jarumi da ya taka gaggarumar rawa a Faransa da wasu kasashe aminan Faransa.

Ko baya ga Louvre, marigayin ya zana gine-gine a sassa daban daban na duniya da suka hada da gidan tarihi na Suzhou a China, da ginin babban bankin China.