Isa ga babban shafi
Birtaniya

Theresa May ta gaza cimma jituwa da jam'iyyar Labour

Bayan kammala tattaunawa tsakanin Theresa May da jam’iyyar Labour ba tare da cimma yarjejeniya ba a jiya Juma’a, sakataren da ke kula shirin ficewar Birtaniyan daga kungiyar Tarayyar Turai EU Keir Starmer ya nemi majalisar kasar ta sake bai wa daidaikun jama’a damar sake kada kuri’a kan kudirin.

Firaministar Birtaniya Theresa May
Firaministar Birtaniya Theresa May REUTERS/Peter Nicholls
Talla

Yayin tattaunawar tsakanin Firaministar da Jam’iyyar Labour wadda aka karkare a jiya, Labour ta tsaya kan bakar ko dai Theresa May ta samar gagaruman sauye-sauye a kunshin yarjejeniyar tata da EU ko kuma ta amince da zaben gaggawa.

Haka zalika Jam'iyyar ta Labour ta yi barazanar cewa matukar duka zabi biyun da ta bai wa Firaministar ba su samu ba, to kai tsaye za ta goyi bayan shirin sake kada kuri’a kan shirin ficewar kasar daga EU.

Firaminista Theresa May dai ta ce, za ta mikawa Majalisar kasar zabi daban-daban duk wanda jama’a suka fi rinjaye kai tsaye shi kasar za ta yi amfani da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.