rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

New Zealand Ta'addanci Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dan ta'addan da ya hallaka masallata 51 ya sake gurfana a Kotu

media
Brenton Tarrant, dan ta'addan da ya hallaka Masallata 51 a New Zealand. Reuters

A karon farko yau talata, ‘yan sanda a kasar New Zealand sun tuhumi dan ta’addan nan da ya harbe Masallata 51 a Masallachi, Brenton Tarrant da aikata laifin ta’addanci.


Sanarwar da yan sanda suka gabatar tace, yanzu haka ana tuhumar Tarrant da aikata laifin ta’addanci a karkashin sashe 6 na dokar ayyukan ta’addanci da kasar ta amince da shi a shekarar 2002.

Yan Sandan sun ce bayan tuhumar aikata lafin ta’addancin, ana kuma tuhumar Tannat da laifin kasha mutane 51 da kuma yunkurin kashe wasu 40.

Harin dai shi ne mafi muni da New Zealand ta taba fuskanta a tarihi.

Masallatan da aka kai harin sun hada da Masallacin Al-Noor mafi girma a birnin Christchurch.

A wani faifan bidiyon harin an ga yadda maharin ke bin wadanda basu karasa mutuwa ba, yana karasa hallaka su.