Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Turai na fargabar shigar mulkin EU hannun masu ra'ayin rikau

Dai dai lokacin da ya rage kwanaki 2 mutane miliyan 400 su fara kada kuri’a a zaben tarayyar Turai da zai gudana a kasashen Nahiyar 28, shugabannin kasashen na ci gaba da jan hankalin al’ummarsu don gudun kada shugabancin majalisar kungiyar ya fada hannun masu tsattsauran ra’ayi.

Tambarin zaben kungiyar Tarayyar Turai na 2019
Tambarin zaben kungiyar Tarayyar Turai na 2019 RFI
Talla

Zaben wanda za a fara ranar Alhamis a kammala ranar Lahadin makon nan, wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a ta nuna yadda jam’iyyun masu kyamar baki ka iya samun gagarumin rinjaye, wanda kuma ke matsayin babban kalubale ga masu tsaka-tsakan ra’ayi, ko da dai wasu na ganin zargin badakalar rashawar shugaban gwamnatin Austria na jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi ka iya sauya hasashen.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda ya jima ya na jan hankali game da illar fadawar mulkin kungiyar ta EU hannun masu tsattsauran ra’ayi, ya ce zaben shi ne mafimuhimmanci da nahiyar za ta gudanar tun bayan 1979 la’akari da yadda sabbin jam’iyyu masu tsattsauran ra’ayi ke kara yaduwa a yankin.

Tun bayan fara zaben shugabancin kungiyar a shekarar 1979, a kowanne lokaci akan fuskanci karancin masu fitowa kada kuri’a a zaben, matakin da shugaba Macron ke cewa dole a kawo karshen matsalar.

Shima dai shugaban majalisar kungiyar ta EU mai barin gado Jean-Claude Junker yayin wani taron kasuwanci da ya gudana a Vienna, ya bukaci al’umma su jajirce akan abin da su ke so yayin zaben na kwanaki 5.

Kasashen Birtaniya da Netherland ne dai sahun gaba da za su fara kada kuri’ar ta su a ranar Alhamis yayinda sauran kasashen kungiyar 26 kuma za su amfani da sauran kwanakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.