Isa ga babban shafi
Birtaniya

Brexit: Theresa May ta sake shiga tsaka mai wuya

Wasu ‘yan Majalisar Jam’iyyar Conservative ta Fira Ministar Birtaniya Theresa May, sun soma tattaunawa kan yiwuwar bayar da damar sake kada mata kuri’ar yankan kauna a yau Laraba.

Fira Ministar Birtaniya Theresa May.
Fira Ministar Birtaniya Theresa May. Kirsty Wigglesworth/Pool/REUTERS
Talla

Matakin na zo a dai dai lokacin da Fira Ministar ke neman sake kada kuri’a karo na 4 kan yarjejeniyar shirin ficewar kasar daga cikin Kungiyar Tarayyar Turai.

Wannan dai ne karo na 2 cikin watanni 5 da Thresa May za ta fuskanci kada kuri’ar yankan kauna daga ‘yan majalisarta, tun bayan watan Disamba da ta sha da kyar, dai dai lokacin da ta ke kokarin bayar da damar sake gudanar da zaben raba gardama kan shirin ficewar kasar daga EU.

Matakin ‘yan majalisar na Conservative 18 na zuwa ne bayan kammala jawaban Theresa May a zauren majalisar yau Laraba, inda ta tabbatar da shirinta na bada damar sake kada kuri’a kan kunshin yarjejeniyar ta da EU karo na 4 ko kuma ba da damar sake kada kuri’ar raba gardama kan shirin ficewar baki daya kamar yadda wasu suka bukata.

Cikin dai masu goyon bayan sake bai wa jama’ar Birtaniya damar sake kada kuri’ar raba gardamar hadda Lan Blackford wanda yace matukar aka sake kada kuri’ar kan yarjejeniyar babu shakka Firaministar za ta yi sha kaye fiye da wanda ta sha sau 3 a baya.

A cewar Blackford, jagoran Jam’iyyar Nationalist a Westminster, babu shakka yarjejeniyar May ta mutu kuma kamata ya yi ta sako daga farko, matukar ta na bukatar goyon baya.

Shima dai jagoran jam’iyyar Labour eremy Corbyn ya yi kakkausar suka kan jawaban na Theresa May, inda ya ce, idan har da Fira ministar ta gamsu da zabin da ta ke kai, bai kamata ta ji tsoron bai wa jama’a damar sake kada kuri’ar raba gardamar ficewar kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.