Isa ga babban shafi
Birtaniya

Firaministar Birtaniya ta sanar da murabus dinta

Firaministar Birtaniya Theresa May ta sanar da murabus dinta, inda ta ce za ta sauka daga shugabancin Jam’iyyar Conservative a ranar 7 ga watan Yuni mai zuwa, lamarin da ya bude fagen takarar neman wanda zai gaje ta.

Firaministar Birtaniya Theresa May
Firaministar Birtaniya Theresa May REUTERS/Toby Melville
Talla

A wani jawabi da ta gabatar cikin yanayi na tausayi, May ta ce, ta yi iya bakin kokarinta a game da ficewar kasar daga Kungiyar Tarayyar Turai, tana mai nadamar gazawarta kan cimma burin ficewar.

Uwargida May ta ce, za ta ci gaba da zama a mukamin Firaministan Birtaniya kafin samun magajinta.

Jam’iyyar Conservative mai mulki ta ce, tana fatan za a samu sabon shugaba nan da karshen watan Yuli mai zuwa.

Wannan na nufin cewa, Uwargida May ce za ta karbi bakwancin shugaban Amurka Donald Trump da zai ziyarci Birtaniya a farkon watan gobe.

Tuni Sakataren Harkokin Wajen kasar Jeremy Hunt ya bi sahun Boris Johnson da Esther McVey da kuma Rory Stewart wajen fafutukar neman shugabancin jam’iyyar ta Conservative.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.