rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Diflomasiya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugabannin Turai za su gudanar da taron farko bayan zabe

media
'Yan majalisar Tarayyar Turai FREDERICK FLORIN / AFP

Kwanaki biyu bayan kammala zaben Majalisar dokokin Turai, a yau shugabannin kasashen yankin za su gudanar da taron farko a birnin Brussels domin tattaunawa kan yadda za a zabi sabo shugaba da kuma na sauran cibiyoyi na kungiyar ta Turai.

To sai dai a wannan karo kamar yadda manazarta ke cewa, nada sabbin shugabannin zai kasance mai sarkakkiya, lura da yadda aka samu bakin fuskoki a sabuwar majalisar.


Babban aikin da ke gaban shugabannin da ke halartar wannan taro shi ne cimma matsaya kan wanda za a nada a matsayin sabon shugaban hukumar gudanarwa na kungiyar ta Turai, mukamin da Jean-Claude Juncker ya share shekaru biyar a kansa.

Karkashin dokokin hukumar ta EU, shugabannin kasashen yankin 28 ne ke zaben shugaban hukumar, kafin daga bisani a gabatar da sunansa gaban majalisar dokoki mai wakilai 751 domin ta tabbatar da shi.

A halin yanzu dai mataimakin Juncker wanda ya fito daga jam’iyyar masu tsaka-tsakan ra’ayi kuma tsohon minista daga kasar Netherland ne Frans Timmermans, ke neman wannan matsayi, kuma ga alama zai samu goyon bayan shugabanni da suka hada da Emmanuel Macorn na Faransa da kuma Angela Melkel ta Jamus,

To sai dai ko shakka babu Timmermans zai fuskanci tirjiya daga wasu kasashen lura da yadda aka samu wakilci daga jam’iyyu masu bambanci ra’ayoyi daga kasashe daban daban na nahiyar ta Turai a wannan karo.