rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Amurka Diflomasiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump ya samu tarba ta musamman a fadar Sarauniyar Ingila

media
U.S. President Donald Trump inspects an honour guard with Britain's Prince Charles at Buckingham Palace, in London, Britain, June 3, 2019. REUTERS/Toby Melville/Pool

Sauraniyar Ingila, Queen Elizabeth ta Biyu, da Yerima Charles ne suka tarbi shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa Melania a fadar Buckingham a yau Litinin, a wata ziyarar kwanaki uku mai cike da shagulgula da cece kuce tare da gardandami da ya fara a Ingila.


Bayan harba bindiga har sau 41 a matsayin karramawa, a wajen fadar Sarauniyar Ingila, bakon na Ingila, shugaba Donald Trump ya yi musabaha da Sarauniya Elizabeth Ta Biyu sannan ya karasa cikin fadar.

Yerima Charles da uwargidarsa Camilla sun bullo daga bayan fadar da ke tsakiyar birnin Landan, don tarbar shugaba Trump da maidakinsa, wadanda suka sauka daga jirgin sama mai saukar ungulu, bayan sun ci zango a ofishin jakadancin Amurka a Landan.

Shugaba Trump da uwargidarsa Melania sun jera tare, inda suka hau matakala, don isa ga inda Sarauniyar take, a kan idon ‘yar Trump Ivanka da mijinta Jared.

Daga nan sai Sarauniyar da iyalan na Trump suka shiga daga ciki, daga bisani suka sake fitowa don sauraron taken Amurka.

An kuma karrama shugaba Trump ta wajen ba shi damar duba faretin sojin Birtaniya, masu sanye da kaya da aka yi musamman don sanyawa a lokacin biki.