rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tennis Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Federer zai karawa da Nadal a wasar dab da na karshe

media
Roger Federer da Rafael Nadal a fagen Tennis Reuters/Montaje RFI

Roger Federer da a shekara da ta gabata ya samu nasarar komawa matsayinsa na lamba daya mafi kwarewa a fagen wasan kwallon Tennis ajin maza a duniya zai fafata da Rafael Nadal a yau juma’a a wasar dab da na karshe a gasar Rolland Garros.


Federer dan kasar Switzerland na samun goyan baya daga sassa daban-daban ganin kwarrewar sa a duniyar Tennis,sai dai Rafael Nadal ba kanwar lasa bane.

Federer ya kafa tarihin zama dan wasan Tennis na biyu a duniya da yafi takwarorinsa yawan lashe kofunan wasannin Tennis, bayan Jimmy Connors dan kasar Amurka da ya lashe kofunan gasar tennis har sau 109, a tsawon lokacin da ya shafe a fagen wasan na tennis.

Rafael Nadal na daga cikin yan wasa da ya kafa tarihi a gasar Roland Garros da ake gudanarwa a Faransa inda ya lashe kofin gasar sau 10.

Nadal ya ce yana cike da farinciki kasancewa zai fafata da Roger Federer a wannan gasa ta Rolland Garros.

A bangaren mata, a yau juma’ yar kasar Austria Ashleigh Barty zata fafata da yar kasar Amurka Amanda Anisimova,karawa ta biyu zata hada yar Birtaniya Johanna Konta da yar kasar Tcheque Marketa Vondrousova.