Isa ga babban shafi
Turai

Trump zai tura dakaru dubu zuwa Poland

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirin tura dakaru 1,000 zuwa kasar Poland domin fuskantar duk wata barazana dake iya tasowa daga Rasha, yayin da ya soki Jamus kan yadda ta bari Rashar tayi garkuwa da ita.

Shugaban Amurka Donald Trump tare da takwaransa na Poland Andrzej Duda.
Shugaban Amurka Donald Trump tare da takwaransa na Poland Andrzej Duda. AFP / MANDEL NGAN
Talla

Babu dai cikakken bayanai kan Karin sojojin 1,000 da za’a kai Poland, wanda ya gaza bukatar shugaba Andrzej Duda na ganin Amurkar ta kafa sansanin soji na dindindin.

Kasar Amurka dama nada sojoji 5,000 a Poland wadanda ke aiki a karkashin kungiyar kawancen tsaro ta NATO, yayin da shugaba Donald Trump yace za’a kwashe sojojin 1,000 ne daga Jamus domin kai su Poland.

A ganawar da suka yi da shugaban Duda, shugaba Trump ya nuna rashin amincewa da kafa sansani na musamman a cikin Poland.

Sakatare Janar na kungiyar NATO Jens Stoltenberg ya bayyana farin cikin sa da matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.