Isa ga babban shafi
Faransa

Tattara kudin gyaran majami'ar Notre-Dame na neman gagara

Rahotanni daga Faransa na nuni da cewa yanzu haka an fara amfani da kudaden da aka tara daga hannun jama’a wajen fara aikin sake ginin Majami’ar Notre-Dame da ke birnin Paris wadda gobara ta lalata watanni 2 da suka gabata.

Wani bangare na Majami'ar Notre-Dame da aka fara aikin sabunta gininsa
Wani bangare na Majami'ar Notre-Dame da aka fara aikin sabunta gininsa REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Sai dai mai Magana da yawun majami’ar Andre Finot ya ce kawo yanzu manyan attajirai ta ‘yan kasuwar da suka yi alkwarin tallafawa basu fara aikewa da kudaden da suka alkawarta ba.

A jiya Asabar ne majami’ar ta yi taron jama’a karon farko tun bayan gobarar ta ranar 15 ga watan Aprilu da ta yi gagarumar banna ga majami’ar mai dogon tarihi.

Tun a juma’ar da ta gabata ne da ministan al’adu na faransa ya bayyana cewa kasa da kashi 10 cikin 100 na kudaden da akayi alkawarin tallafawa don sake ginin majami’ar kadai aka hada, galibi kuma kudaden sun fito ne daga masu karamin karfi da daidaikun jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.