Isa ga babban shafi

Macron ya bukaci Iran ta kara hakuri kan yarjejeniyar nukiliyarta

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci Iran ta kara hakuri tare da dattaku, bayan ta ce za ta ninka aikin samarwa, tare da tace makamashin nukiliyarta da take tarawa, har sai ta zarce iyakar da aka mata, karkashin yarjejeniyar da ta kulla da manyan kasashen Turai a shekarar 2015.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Francois Mori/Pool via REUTERS
Talla

Sanarwar yin watsi da yarjejeniyar nukiliya da Iran ta bayar ta zafafa matsin lamba kan batun, tun bayan da Amurka ta janye daga yarjejeniyar a shekarar da ta gabata.

Macron ya ce idan fa rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya ya munana, ba zai tsinana wa kowa komai ba, saboda la shakka, zai bata wa Iraniyawa da ma sauran kasashen duniya rawarsu da tsalle, don haka ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen rinjayar Iran zuwa ga jingine shawararta.

Amurka ta zargi Iran da kai hari kan wasu tankokin mai a tekun Oman, a makon da ya gabata, zargin da Iran ta ce ba shi da tushe ballantana makama.

Shugaban na Faransa dai ya yi kaffa - kaffa wajen yin tsokaci game da wannan batu, yana mai cewa dole sai an kammala tattara bayanai game da harin da aka kai wa tankokin mai a teku kafin a ayyana wani a matsayin mai laifi.

Ya kara da cewa, wannan yanayi da ake ciki yana bukatar a yi sara ana duban bakin gatari, saboda haka abu ne mai amfani a kasance a natse.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.