rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Canjin Yanayi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen EU na shirin kawar da sinadarin Carbon nan da shekarar 2050

media
Tiriri da gurbataccen hayaki mai haddasa dumamar yanayi REUTERS/Vincent West (SPAIN) -/File Photo

Shugabannin kungiyar kasashen Turai sun sha alwashin kawo karshen sinadarin iskar Carbon mai haddasa dumamar yanayi nan da shekarar 2050, matakin da ke zuwa bayan zaben Tarayyar Turan wanda ya gudane cike da fargabar gaza samar da mafita kan sauyin yanayi.


Wasu bayanai daga kungiyar Turan ta EU na nuni da cewa taron shugabanninta da zai gudana tsakanin ranakun Alhamis zuwa Juma’a a Brussels zai mayar da hankali kan yadda za a magance matsalar dumamar yanayi ta hanyar daura damarar kawo karshen iskar ta Carbon dungurugum nan da shekara ta 2050.

Yanzu haka dai wasu kasashen na EU 16 daga cikin 28 tare da hadin gwiwar kungiyar muhalli ta duniya sun hada hannu wajen ganin an rage sinadaran da ke haddasa matsalar ta dumamar yanayi.

Wata majiya ta bayyanawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, yayin taron na kwanaki biyu za a tafka muhawara tsakanin shugabanin na EU wanda kuma ake ganin akwai yiwuwar a samu karin masu mara baya ga shirin yaki da dumamar yanayi.

Cikin wata sanarwa da EU ta fitar ta nuna cewa matsalar dumamar yanayi ta fara bayyana ta yadda kowa zai iya ganinta a yanzu haka, matakin da ke nuna cewa ya zama wajibi a mike tsaye a yakin da ake da matsalar.

A cewar majiyar ta EU babbar matsalar da ta haddasa Tirjiyar wasu kasashe da suka ki amincewa da shirin yaki da dumamar yanayin bai wuce matsalar tattalin arziki ba, wanda kuma a yanzu haka an samar da mafita ga matsalar.