rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Ukraine Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Majalisar Turai ta dawo da 'Yan Majalisun Rasha zaurenta

media
Shugaban Rasha Vladimir Putin 路透社。

Majalisar Tarayyar Turai ta amince da shirin dawo da Yan Majalisun Rasha zuwa cikin ta, shekaru 5 bayan dakatar da su da kuma sanya kasar takunkumi, sakamakon mamaye Yankin Crimea.


Duk da adawar da Ukraine ke yi da matakin, Yan Majalisu 118 suka amince da bukatar dawo da Rasha cikin ta, yayin da 62 suka ki, kana 10 suka ki kada kuri’a.

Dakatar da Rasha daga Majalisar ya sanya ta dakatar da kudaden da take biya da suka kai Dala miliyan 37 daga shekarar 2017, yayin da tayi barazanar ficewa daga Majalisar baki daya.

Sakariyar kula da harkokin kasashen Turai a Faransa, Amelie de Montchalin ta ce ya na da hadari a hana miliyoyin mutane damar zama cikin kungiyar.