rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Lafiya Shari'a

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An saki likitan da ya kashe iyalansa bayan shekaru 20

media
Jean-Claude Romand, a lokacin shari'ar sa ranar 25 ga watan Afrelun 1996. Philippe DESMAZES / AFP

Mahukuntan Faransa sun saki wani likitan bogi da ya kashe mahaifan sa da matar sa da yaran sa lokacin da yayi karyar cewar shi kwararen likita ne kuma ya kwashe shekaru 20 yana aiki kafin a gano shi.


An saki mutumin mai suna Jean-Claude Romand mai shekaru 65 ne daga gidan yarin Saint-Maur dake tsakiyar Faransa bayan ya kwashe shekaru 26 a gidan yari.

Shidai Romand da aka bayyana shi a matsayin daya daga cikin mutanen da suka fi aikata kisa a Faransa da gangan ya kashe iyayen sa da matar sa da kuma yaran sa guda biyu a shekarar 1993 domin kada su gano cewar shi likitan bogi ne wanda ya kwashe shekaru 20 yana aiki.