rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan sandan Faransa na shan suka kan azabtar da masu zanga-zanga

media
Wasu 'yan sandan Faransa lokacin da su ke dakile masu zanga-zanga a birnin Paris REUTERS/Philippe Wojazer

'Yan Sandan Faransa na fuskantar matukar suka kan yadda faifan bidiyo ya nuna jami’an su na fesa hayaki mai yaji kan masu fafutukar kare muhalli da ke zaman dirshan wajen wata gada a birnin Paris.


Ministan cikin gida Christophe Castaner ya bukaci gudanar da bincike kan lamarin da ya auku ranar juma’a lokacin da masu zanga zangar ke nuna rashin gamsuwar su da manufofin gwamnati.

Hotunan bidiyon da aka nada wanda aka yada ta kafar intanet da kuma tashoshin talabijin sun haifar da mumunar suka kan jami’an Yan Sandan.