rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

A karon farko mata za su jagoranci shugabancin EU

media
Ursula von der Leyen da aka amince ta shugabanci Hukumar Tarayyar Turai REUTERS/Michael Kappeler

Shugabannin kasashen Turai sun cimma matsaya a taron da suka gudanar a birnin Brussels, inda a karon farko suka amince da matakin mika manyan mukaman Kungiyar Tarayyar Turai a hannun mata biyu.


Bayan shafe kwanaki uku suna kai ruwa rana a tsakaninsu, shugabannin kasashen Turai sun amince da nadin Ministar Tsaron Jamus, Ursula von der Leyen domin maye gurbin Jean Claude Juncker da ya shafe shekaru biyar yana jagorantar Hukumar Tarayyar Turai.

Da zaran an tabbatar da ita, von der Leyen za ta jagoranci Hukumar Turai wadda ke fama da tarin kalubale da suka hada da matsalar dumamar yanayi da yada labaran karya da tsattsauriyar akida da kuma ficewar Birtaniya daga gungun kasashen yankin.

An dai amince da nadin von der Leyen ce ta jam’iyyar Conservative bayan adawar da aka nuna wa Frans Timmermans na jam’iyyar Socialist daga kasar Netherland.

A bangare guda, tsohuwar Ministar Kudin Faransa, Christine Lagarde wadd ta shugabanci Asusun Lamuni na Duniya, IMF, ita ce a wannan karo za ta jagoranci Babban Bankin Kasashen Turai.

Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai da ya karbi bakwancin taron, Donald Tusk ya tabbatar da nadin matan biyu a manyan mukaman, abinda ya kawo karshen kiki-kakar da ta mamaye taron shugabannin na Turai 28 a Brussels.