rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen Turai sun gaza zaben sabon shugaban EU

media
Wasu daga cikin shugabannin kasashen Turai ©REUTERS/Yves Herman

Shugabannin kasashen Turai sun gaza cimma matsaya a daidai lokacin da suka shiga kwanaki uku na tattaunawa game da cike guraben manyan mukaman kungiyar tarayyar Turai. Rarrabuwar kawanan da ake samu a tsakanin kasashen na yin barazana game da cimma matsayarsu ta zaben sabon shugaban kungiyar cikin gaggawa.


Kasashen sun tashi baram-baram a zaman sa’o’i 18 da suka gudanar a ranar Litinin, inda kasashen Jamus da Faransa suka ki cimma matsaya kan wanda zai zama sabon shugaban Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai .

Sai dai wata majiya ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, a halin yanzu, kasashen na Jamus da Faransa na kan gudanar da tattaunawa a tsakaninsu domin amincewa da Ministar Tsaron Jamus, Ursula von de Leyen na jam’iyyar Conservative a matsayin 'yar takarar da za su mika mata ragamar kungiyar.

Dan takarar da suka mara wa baya a farko, wato Frans Timmermans na jam’iyyar Socialist daga Netherland, na ci gaba da fuskantar adawa a wannan Talata.

Firaministan Jamhuriyar Czech, Andrej Babis ya soki Timmermans, yana mai cewa, sam kasashen yankin gabashin Turai ba za su amince da shi ba, abinda ya haddasa zazzafar muhawarar sirri.

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta gargadi cewa, akwai bukatar kowannensu ya fahimci cewa, ya kamata su samu ci gaba dangane da wannan kiki-kakar.