rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Pakistan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa ta mayarwa Pakistan kayayakin tarihi kusan 450

media
Kayan tarihi da aka nuna a wani biki RFI/Isabelle Le Gonidec

Kasar Faransa ta mikawa Pakistan kayayakin tarihi kusan 450, wasun su da akayi su tun a karni na 4 da hukumomin kwastam suka kwace sama da shekaru 10.


Hukumar kwastan a tashar jiragen Charles de Gaulle dake birnin Paris ta kwace kayayakin a shekarar 2006 lokacin da ake kokarin safarar su.

Bayan binciken da hukumomi suka yi da kuma kai samame gidajen aje kayan tarihi a Paris, anyi nasarar kwace irin wadanan kayan tarihi 445 wanda aka mikawa jamiā€™an diflomasiyar Pakistan.