rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa ta yi na'am da cinikin bai - daya tsakanin Canada da Turai

media
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Koji Sasahara/Pool via REUTERS

Gwamnatin Faransa ta amince da yarjejeniyar cinikin bai daya tsakanin kasar Canada da kasashen Turai, CETA, a wata yarjejeniya mafi girma da nahiyar zata kulla da wata akasa a Arewacin Amurka, wadda majalisar Turai zata kada kuri’a a kai a watan gobe.


Karamin ministan harkokin wajen Faransa Jean-Baptiste Lemoyne, ya bayyana hakan, inda yace, majalisar ministocin kasar ta amince da hakan bayan zazzafar muhawara da bangarorin da ke adawa da shirin.

Ministan ya ce, yarjejeniyar wucin gadi da ta soma aiki, shekaru biyu da suka gabata a matsayin gwaji na da tasiri.

yace, hajojin da Faransa ke fitar da su zuwa Canada ya karu da sama da kashi 6 tsakanin shekarar 2017-2018.

Shima shugaban Faransa Eammanuel Macron, a wani taron manema labarai da Frimministan Canada Justin Trudeau, a watan jiya, yace, yarjejeniyar gwajin tayi nasara.

Ita dai wannan yarjejeniyar Tattalin Arziƙi da Harkokin Cinikayya (CETA) zata bada dama ga kussan duk kayayyaki da ake hada-hadarsu tsakanin kasashen Turai da Canada, ba tare da biyan kudin Custom ba, wadda Turai din ta kiyasta ana kashe kimanin Euro miliyan 590 ko wace shekara.

Majalisar Turai dai ta amince da wannan yarjejeniyar, to amma sai daukacin kasashe mambobin kungiyar EU sun amince kafin ta zama ta din-din-din.