rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sabuwar shugabar EU ta gana da takwarorinta masu barin gado

media
Ursula von der Leyen, zababbiyar shugabar majalisar zartaswar kungiyar tarayyar Turai, kuma ministan tsaron kasar Jamus. Reuters

A karo na farko, zababbiyar yar takarar kasashen turai 28, kan mukamin shugabancin majalisar zartaswar kungiyar tarayyar Turai, ministan tsaron kasar Jamus, Ursula von der Leyen, ta gana da shuwagabanin Kungiyar Jean-Claude Juncker da Donald Tusk.


Ursula Von der Leyen, tace makasudin tattakin shi ne ganawa da shugaban kungiyar mai barin gado Jean-Claude Junker, don samun ingantattun shawarwari, kan tafiyar da kungiyar ta EU na shekaru biyar masu zuwa.

Von ta wallafa a shafinta na Twitta, cewar abin da tafi maida hankali kai a yanzu, shi ne neman shawara da kuma sauraron dukkan bangarorin majalisar ta Turai.

Von der Leyen da ke shirin darewa jagorancin Turai a matsayin mace ta farko a tarihi, dole ne sai ta samu goyon bayan dukkan bangarorin majalisar Turai kafin hakarta ta cimma ruwa.