Isa ga babban shafi
Girka

Jam'iyyar adawa ta lashe zaben shugabancin Girka

Fira ministan Girka mai jiran gado Kyriakos Mitsotakis ya sha alwashin sanya kasar cikin sahun gaba wajen samar da ayyukan yi da tsaro da kuma cigaba bayan samun gagarumar nasara a zaben Yan Majalisun kasar da aka yi jiya.

Sabon Fira Ministan Girka Kyriakos Mitsotakis.
Sabon Fira Ministan Girka Kyriakos Mitsotakis. AFP
Talla

Hukumar zaben Girka ta bayyana Kyriakos Mitsotakis a matsayin wanda ya samu gagarumar nasara kan Fira minista mai barin gado, Alexis Tsipiras wanda ya jagoranci kasar wajen fitar da ita daga matsalar tattalin arziki.

Alkaluman hukumar da aka sanar sun ce Jam’iyyar New Democracy ta Mitsotakis ta samu kusan kashi 40, yayin da Jam’iyyar Tsipiras ta Syriza ta samu kashi 31 da rabi.

A jawabin da ya yiwa al’ummar kasar ta kafar talabijin, Mitsotakis ya bayyana cewar an rufe babin shan wahala a kasar, inda yake cewa Girka zata sake daga kafadar ta a karkashin mulkin sa.

Zababben Fira ministan mai jiran gado ya shaidawa al’ummar kasar cewar ba zai gaza wajen aiwatar da bukatun jama’a ba.

Yau ake saran rantsar da Mitsotakis a karagar mulki, yayin da Tsipiras ya amsa shan kaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.