Isa ga babban shafi
Duniya

Jakadan Birtaniya a Amurka ya yi murabus

Jakadan Birtaniya a Washington Kim Darroch ya sanar da aje aikin sa bayan cacar bakin da aka samu tsakanin shugaba Donald Trump da shugabannin Birtaniya kan wani rahotan asiri da ake zargin sa da rubutawa, inda ya bayyana shugaba Trump a matsayin sakarai mara kan gado.

Kim Darroch tsohon jakadan Birtaniya a Amurka
Kim Darroch tsohon jakadan Birtaniya a Amurka Paul Morigi / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP
Talla

Firaminista mai barin gado Theresa May ce ta sanar da murabus din Jakada Kim Darrock lokacin da take jawabi a zauren majalisar dokoki, inda ta bayyana matakin a matsayin abin takaici.

Shugaba Donald Trump ya bayyana Darroch a matsayin mara hankali wanda ba a bukatar sa a Amurka, yayin da ita ma Firaministar Birtaniya Theresa May bata tsira daga shugaban na Amurka ba, wanda ya zargi manufofin gwamnatin ta.

Duk da wannan cacar bakin, gwamnatin Birtaniya tace tana goyan bayan Jakadan nata mai barin gado, dari bisa dari, saboda yadda yake gudanar da ayyukan sa, kamar yadda Sakataren harkokin waje Jeremy Hunt ya bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.