rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yar sarkin Makka ta gurfana a kotun Faransa kan dukan ma'aikacinta

media
Gimbiya Hassa bint Salman, 'yar uwa yarima mai jiran gado na Saudiya na Saudiya Muhammad bin Salman Arab.com

Hukumomin Kasar Faransa sun gurfanar da 'yar uwar Yarima Muhammad bin Salman a gaban kotu saboda tuhumar da ake mata na dukan wani ma’aikacin da ke mata gyara a gidan ta na alfarma da ke birnin Paris.


Ana tuhumar Gimbiya Hassa bin Salman wadda ‘ya ce ga Sarki Salman bin Abdulaziz da sanya mai tsaron lafiyar ta Rani Saidi da dukar Ashraf Eid lokacin da aka same shi ya na daukar hotan katafaren gidan a shekarar 2016.

Hassa dai ba ta gurfana a kotu ba yayin sauraren karar, amma lauyan ta ya ce taki amincewa da tuhumar da ake mata.