rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Spain Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Fira ministan Spain na fafutukar kafa gwamnatin kawance

media
Pedro Sánchez Firaministan Spain a wata ganawa da manema labarai Fuente: Reuters.

Yayi da ya rage wa’adin makwanni biyu a sake gudanar ad zaben yan Majalisu a Spain, Firaministan rikon kasar Pedro Sanchez na cigaba da kokarin kafa gwamnatin kawancen domin kaucewa zuwa zabe.


Jam’iyyar Sanchez ta samu kujeru 123 daga cikin kujeru 350 dake Majalisar a zaben da akayi a watan Afrilu, abinda ya hana ta samun rinjayen kafa gwamnati.

Bayan yunkurin sa na kulla kawancen kafa sabuwar gwamnati ya gagara, Firaministan ya sanya ranar 23 ga watan nan a matsayin ranar gudanar da sabon zabe, amma kuma hakan bai hana shi cigaba da tuntubar wasu Jam’iyyu ba domin kaucewa zuwa zaben.