Isa ga babban shafi
Faransa

Ana bukukuwan zagayowar ranar 'yanci a Faransa

Sojoji sama da dubu hudu ne ke gudanar da faterin zagayen ranar 14 ga watan Yuli a kan titin Champs Elysees da ke birnin Paris, a daidai lokacin da Faransawa ke gudanar da bukukuwan zagayowar ranar ‘yanci a wannan lahadi.

Bukukuwan ranar 'yanci a Faransa
Bukukuwan ranar 'yanci a Faransa Philippe Lopez, AFP
Talla

Wasu daga cikin sojojin da ke faretin sun hada da na Faransa da Jamus da ke aikin bayar da horo a kasar Mali, sannan an tsara faretin a cikin motoci 196, dawaki 237, jiragen yaki 67 da kuma wasu jiragen masu saukar angulu 40 da za su yi shawagi.

Ana gudanar da bikin ne a gaban idon shugaba Faransa Emmanuel Macron da kuma Angela Merkel ta Jamus, yayin da Theresa May tura mataimakinta David Lidington domin ya wakilce ta sai kuma shugaban Majalisar Hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker.

Emmanuel Macron na fatan yin amfani da bikin na bana ne domin kara samar da hadin-kai tsakakin kasashen Turia, a daidai lokacin dai Birtaniya ta yanke shawarar ficewa daga cikin wannan gugun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.