Isa ga babban shafi
Faransa

Zanga-zanga ta biyo bayan faretin bikin ranar Bastille

Jim kadan bayan kammala faretin bikin zagayowar ranar Bastille da Faransawa suka yi juyin juya hali, arrangama ta barke tsakanin jami'an tsaro da kungiyar masu sanye da rigunan dorawa da ke zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin shugaba Emmanuel Macron a birnin Paris.

Wani yanki a gaf da fadar shugaban Faransa ta Champs Elysee, yayin arrangama tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda.
Wani yanki a gaf da fadar shugaban Faransa ta Champs Elysee, yayin arrangama tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda. AFP
Talla

Arrangamar ta auku ne a gaf da fadar shugaban kasa da ke Champs-Elysees, lokacin da masu zanga-zangar suka soma kayar da shingayen da aka kafa don baiwa faretin da ya gudana kariya, tare da cinnawa wuraren zubda shara wuta a tituna, yan sanda kuma suka afka musu da barkonon tsohuwa.

Yau Faransa ta gudanar da bikin zagayowar ranar Bastille da yan kasar suka yi juyin juya halin da kawo karshen mulkin sarakunan gargajiya a rana mai kamar ta yau, 14 ga watan Yuli a 1789.

Bikin da aka soma da misalin karfe 10:30 na safe a Paris, ya gudana ne a karkashin jagorancin shugaban Faransa Emmanuel Macron, da sauran takwarorinsa na kasashen Turai, ciki harda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Akalla jami’an tsaro da suka hadada sojoji, yan sandada Jandarmomi dubu 4 da 300 ne suka gudanar da Fareti a yau, tareda ababen hawa 196, dawakai 237, jiragen yaki 69 da kuma jirage masusaukar ungulu 39.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.