rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Amurka Donald Trump Hakkin Mata Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump ya sake muzanta 'yan majalisun Amurka mata

media
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Kevin Lamarque

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake jaddada matsayinsa kan ‘yan majalisun kasar mata guda 4 dake cigaba da sukar manufofinsa, inda yace idan basu gamsu da rayuwa a Amurka ba, su fice su koma kasar su.


Yayin jawabi a fadar shugaban kasa, Trump ya bayyana ‘yan majalisun a matsayin gwanayen korafi, wadanda basa son Amurka, sun kuma tsani kasar.

Donald Trump kan muzanta 'yan majalisun Amurka mata 16/07/2019 - Daga Bashir Ibrahim Idris Saurare

Sai dai duk da kalaman na Trump, ‘yan majalisun wakilai 4 da shugaba Donald Trump ya bukaci su koma kasarsu ta asali sun bayyana cewar babu wanda ya isa ya hana su fadin albarkacin bakinsu, bayan da shugaban ya ci gaba da sukar manufofinsu.

Alexandria Ocasio-Cortez da Ayyana Pressley da Rashida Tlaib da kuma Ilhan Omar sun kare sukar shugaban da suke inda suka nesanta manufarsu da zargin da yake musu na nuna wariyar jinsi.

Yan majalisun da suka bayyana matakin shugaban a matsayin yunkurin kawar da kai kan abinda yake faruwa, sun ce zasu ci gaba da ayyukansu kamar yadda suka saba.