Daya daga cikin Ministocin Faransa ya ajiye aiki
Ministan Muhallin Faransa Francois de Rugy, ya yi marabus daga mukaminsa, biyo bayan zargin sa da kashe makudan kudade domin shirya wata liyafar cin abinci da kuma kawata gidansa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Francois de Rugy tsohon minmistan Muhallin Faransa da ya kama aiki a watan Satumbar shekarar 2018, ya sauka daga mukamin sa ne biyo bayan zargin wasa da dukiyar kasar kamar dai yada jaridar kasar mai tonon silili Mediapart tayi masa a makon jiya a shafinta na Intanet.
Jaridar ta wallafa hotunan sa tare da uwargidarsa wadda ‘yar jarida ce a wata liyafar cin abincin dare, ya kuma shirya tareda shirya wasu shagulgula daban.
Cikin zargin da jaridar ke yiwa Francois De Rugy, harda wadda matarsa ta sayi na’urar busar da gashi na kudin EURO 500, kwatankwacin Naira dubu dari biyu, sai kuma gyaran gidan gwamnati da suke ciki da ya lakume EURO dubu 63.
Tsohon Ministan wanda na hannun daman shugaban kasar ne Emmanuel Macron, kuma na biyu a girman mukami fiye da Firaminista, Edouard Philippe, ya ce ya yi marabus din ne sakamakon yadda kafafen yada labarai ke amfani da wannan batu domin cin zarafinsa da kuma na iyalansa.
Francois De Rugy ne Ministan na 11 a Faransa cikin dan karamin lokacin da ya ajiye aikin sa tun bayan zaben Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Elisabeth Borne Ministan sufurin Faransa ce ta maye gurbin sa a cewar wata sanarwa daga fadar gwamnatin kasar ta Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu