rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Amurka Donald Trump Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Majalisar wakilan Amurka ta caccaki Trump kan kalaman wariya

media
Ayanna Pressley, Ilhan Omar, Rashida Tlaib da kuma Alexandria Ocasio-Cortez, 'yan majalisun wakilan Amurka 4 da Donald Trump ya muzanta. REUTERS/Erin Scott

Zauren majalisar wakilan Amurka, ya yi Tur da shugaba Donald Trump kan yadda ya muzanta wasu ‘yan majalisun wakilan kasar mata, ta hanyar amfani da kalaman nuna wariya da kaskanci kansu, da kuma bakin-haure da yan gudun hijira mazauna kasar.


Yan majalisun wakilan Amurka na jam’iyyar Democrats 235 da kuma wasu na Jam’iyyar Republican guda 4 ne suka yi Tur da matakin na shugaba Trump da suka ce zai karfafawa masu nuna wariyar jinsi da kyama ga baki mazauna kasar gwiwa.

Jam’iyyar Democrats ke da rinjaye a zauren majalisar wakilan Amurka mai kujeru 435, amma a majalisar dattijan kasar Republican ke kan gaba, abinda yasa ake ganin da wuya zauren majalisar yayi A Wadai da kalaman na Donald Trump a dunkule.

Uku daga cikin ‘yan majalisun wakilan da Trump ya muzanta saboda sukar manufofinsa, balarabiya, Hispanic, da kuma Ba’amurkiya bakar fata, an haife su ne a Amurka da suka hada da Alexandria Ocasio-Cortez, Rashida Tlaib, da Ayanna Pressly, amma Ilhan Omar ‘yar kabilar Somali, an Haife ta ne a birnin Mogadishu na Somalia ta kuma samu zinin zama a Amurka a 1995.

Ko a farkon makonnan sai da Shugaban Amurka Donald Trump ya sake jaddada matsayinsa kan ‘yan majalisun kasar mata guda 4, inda yace idan basu gamsu da rayuwa a Amurka ba, su koma kasarsu.