rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An gano jirgin ruwan da ya yi hatsari shekaru 51 da suka gabata

media
Jirgin Minerve na Faransa da ya yi hatsari shekaru 51 da suka gabata (Photo by Keystone-France/Gamma-Rapho via Getty Images)

Masu bincike sun gano jirgin karkashin teku mallakin Faransa da ya yi batan-dabo tun shekarar 1968 a yankin yammacin tekun Mediterranean, abinda ya kawo karshen zaman shekaru 51 da iyalan mamatan jirgin suka shafe suna neman bahasi game da aukuwar mummunan hatsarin jirgin a wancan lokaci.


Jim kadan da gano jirgin, Ministar Tsaron Faransa, Florence Parly ta bayyana a shafinta na Twiter cewa, wannan wata nasara ce, kuma samun sukuni ne da kwarewa, yayinda ta ce, tana tunanin iyalan mamatan da suka dauki dogon lokaci suna dako.

A ranar 17 ga watan Janairun shekarar 1968 ne, jirgin karkashin ruwan dauke da matuka 52 ya yi batan-dabo daga gabar ruwan kudancin tekun Faransa.

A farkon wannan shekarar ne, Ministar Tsaron ta Faransa ta sanar da kaddamar da sabuwar tawagar bincike da kunshi kwararru kan sha’anin teku domin sake wani yunkurin karshe na lalubo jirgin biyo bayan kaimin da iyalan mamatan suka kara game da neman bahasi.

An yi amfani da wani jirgin ruwa mallakin kamfanin Amurka mai zaman kansa wajen gano jirgin karkashin teku mai suna Minerve wanda nutsewarsa ta kai mita dubu 2 da 370 kwatankwacin takun-kafa dubu 7 da 800.

Tun a ranar Talatar makon jiya ne, tawagar kwararrun binciken dauke da manyan kamarori ta isa wurin da jirgin karkashin tekun ya yi hatsari.