rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Canjin Yanayi Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tsananin zafi ya tilasta rufe tashar nukiliyar Faransa

media
Jami'an lafiya a Turai sun gargadi masu kanana da yawan shekaru su kaucewa yawo da tsakar rana don kaucewa buguwar tsananin zafi. AFP/File/Miguel MEDINA

Kasar Faransa tare da kasashen da ke Yammacin Turai na shirin fuskantar matsanancin zafi abinda ya kai ga rufe tashar samar da makamashin nukiliyar Faransa.


Masu hasashen yanayi sun ce alkaluman yanayi sun nuna karuwar yanayin zafin da zai kai maki 40 a kasahsen Belgium da Luxembourg da Netherlands, yayin da kuwa zai zarce haka a Faransa, inda ake saran zai kai maki kusan 40 da rabi.

Kamfanin kula da makamashin nukiliya na Faransa yace a wannan talata zai rufe tashar nukiliyar saboda yanayin zafin.

A karshen watan Yuni da ya gabata Faransa ta fuskanci yanayi mafi zafi cikin shekaru sama da 10, bayanda matakin zafin a ma’aunin Celsius ya kai digiri 44.3 a sassan kasar.

Tsananin zafin ne kuma ya tilasta rufe akalla makarantu dubu 4000 a sassan kasar ta Faransa don gudun sake fuskantar rasa rayukan da aka yi a kasar cikin shekarar 2003, inda akalla mutane dubu 15 suka halaka.