Isa ga babban shafi

Boris Johnson ya nada sabbin ministocin sabuwar gwamnatinsa

Sabon Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya bayyana sunayen ministocinsa, inda ya maye gurbin akasarin wadanda ke gwamnatin domin cimma manufar sa ta ficewa daga kungiyar kasashen Tarayyar Turai nan da ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa.

Sabon Fira Ministan kasar Birtaniya Boris Johnson
Sabon Fira Ministan kasar Birtaniya Boris Johnson REUTERS/Toby Melville
Talla

Jim kadan bayan kama aiki a matsayin sabon Firaminista, Boris Johnson sake jaddada matsayin sa na aiwatar da alkawarin da ya yi wa jama’ar kasar cewar, Birtaniya za ta fice daga kungiyar Turai ranar 31 ga watan Oktoba, kafin daga bisani ya fara bayyana sunayen mutanen da ya nada a matsayin ministoci.

Sabbin ministocin na Johnson sun hada da Dominic Rabb wanda zai rike mukamin ministan harkokin waje, sai kuma Sajid Javid a matsayin ministan kudi, yayin da Priti Patal za ta rike mukamin ministan cikin gida.

Sauran ministocin sun hada da Ben Wallace, ministan tsaro, Amber Rudd, ministan ayyuka da fansho, da Lis Truss, ministan kasuwancin kasashen duniya, sai kuma Stephen Barclay, ministan Brexit.

A yau Alhamis ne dai ake saran sabuwar majalisar ministocin ta gudanar da zaman ta na farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.