rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Faransa Jamus

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tsananin zafi na ci gaba da addabar sassan Turai

media
Tsananin zafi ya tilastawa jama'a linkayar dole cikin ruwa. Ouest-France

Tsananin zafin ranar da ke addabar miliyoyin alúmmar kasashen yammacin Turai na ci gaba da habbaka a tsakanin kasashen, inda a birnin Paris na Faransa, zafin ya zarta maki 42 kan ma’aunin Celsius, wanda aka bayyana cewa zai iya karuwa nan da karshen mako.


Kamar yadda aka za ta yanayin zafi a manyan biranen Faransa ya zarta yadda aka saba gani a cikin shekaru 70 da suka gabata a tarihi.

A sauran sassan Turai kuwa, zafin a Belgium ya kai matakin digiri 40 sai kuma Jamus da zafin ya kai digiri 41.5 a ma’aunin Celsius.

Cibiyar hasashen yanayin Jamus ta yi gargadin cewa hasashen tsananin zafin na wucin gadi ne, domin kuwa zai iya zarta yanayin da ake gani.