rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dan bindiga ya bude wuta kan taron bajakolin abinci

media
Filin bajakolin abincin da ke gudana a Jihar California da dan bindiga ya budewa mahalarta wuta. AFP

Wani Dan Bindiga a Amurka ya bude wuta kan mai uwa da wabi wajen wani bikin bajekolin abinci dake gudana a Jihar California, yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane 3.


Hotunan bidiyon da tashar talabijin din NBC ta nuna na dauke da yadda mutane suka ranta a na kare domin tsira da rayukan su daga wajen bikin dake kudu maso gabashin San Jose.

Wata shaidar gani da ido Julissa Contreras ta bayyana cewar wami matashi farar fata ne dake dauke da bindigar ya bude wuta.

Shugaba Donald Trump ya bayyana cewar jamiā€™an tsaro ba suyi nasarar kama dan bindigar ba.