Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

EU na kada kuri'a a zaben wanda zai maye gurbin Lagarde a IMF

Gwamnatocin kasashen kungiyar EU sun fara kada kuri’a a zaben wanda zai jagoranci asusun bada lamuni na duniya IMF a wani sabon tsari da ba safai aka saba ganin irinsa ba, wanda ke da nufin magance banbanbance-banbancen da ke haddasa rarrabuwar kan mambobin kungiyar.

Tsohuwar shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF, Christine Lagarde
Tsohuwar shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF, Christine Lagarde Reuters
Talla

Matakin fara neman wanda zai shugabancin asusun bada lamunin na duniya IMF wanda bisa yarjejeniya tsakanin Tarayyar Turai da Washington yankin ke bayar da shugaba, ya zo ne bayan da da Christine Lagarde ta zama shugabar bankin Tarayyar Turai cikin watan jiya.

Zaben wanda ya zo da sabon tsari a wannan karon za a shafe juma’ar mako 3 ana gudanar da shi tsakanin ‘yan takara guda 3 dukkaninsu daga kudancin nahiyar Turai da suka hadar da tsohuwar ministar kudin Holland Jeroen Dijsselbloem da shugaban babban bankin Finland Olli Rehn da kuma babban jami’i na biyu a bankin duniya Kristalina Gergieva dan kasar Bulgaria.

Ministan Kudin Faransa Bruno Le Maire, dai shi ke jagorantar kokarin hada kan al’ummar yankin wajen ganin ba a samu rarrabuwar kai game da mukamin ba bayan da shugabancin EU ya gaza fitar da wakilcin dan takara guda, da zai jagoranci asusun na bada lamuni da ke birnin Washington na Amurka.

Gabanin fara kada kuri’a tsakanin ‘yan takarar 3 a yau Juma’a Spain ta sanar da janye ‘yar takararta Nadia Calvano matakin da ta ce na da nufin kara hada kan kasashen haka zalika shi ma ministan Kudin Portugal Mario Centeno ya janye, inda a bangare guda shima Gwamnan babban bankin Ingila Mark Carney haifaffen Canada da ake saran ya shiga sahun ‘yan takarar ya sanye da janye aniyarsa, duk dai a wani mataki na neman hadin kan kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.