rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wani Bafaranshe ya kera injin tashi sama mai tsananin gudu

media
Franky Zapata akan sabon injin tashinsa da yiwa suna da Zapata Flyboard REUTERS/Yves Herman

Wani Bafaranshe Franky Zapata da ya shafe shekaru ya na kera wani injin tashi sama da ya kira da Flyboard a turance, ya yi nasarar tashi a yau Lahadi inda a safiyar yau ya yi nasarar tafiyar mill 22 a sararin samaniya bisa rakiyar jirage masu saukar ungulu guda 3.


Da misalin karfe 8 da da mintuna 17 ne Zapata ya yi nasarar tashi akan injin na sa, inda ya yi tafiyar mintuna 22 a sararin samaniya, kafin daga bisani ya sake tashi tun daga kasar ta Faransa zuwa Birtaniya.

Rahotanni sun bayyana cewa Injin tashi saman na Zapata na gudun kilomita 160 zuwa 170 a sa’a guda.

10 da suka gabata dai Zapata ya yi nasarar tashi a kan injin na sa amma kuma ya yi rashin nasarar fadawa teku.