Isa ga babban shafi
Amurka

Trump yayi tur da masu akidar fifita farar fata da kyamar baki

Shugaban Amurka Donald Trump yayi amfani da kakkausan harshe wajen sukar masu akidar fifita turawa farar fata da kuma masu kyamar baki da nuna wariyar launi.

Shugaban Amurka Donald Trump, tare da mataimakinsa Mike Pence.
Shugaban Amurka Donald Trump, tare da mataimakinsa Mike Pence. REUTERS/Leah Millis
Talla

Trump, wanda karo na farko kenan da ya yi tur da masu munanan akidun a bainar jama’a, ya bukaci zartas da hukuncin kisa cikin gaggawa kan duk wanda aka samu da laifin yiwa mutane kisan gilla.

Jawabin na shugaban Amurka a fadar White House yau litinin, martani ne kan kisan gillar da wasu ‘yan bindiga suka yiwa mutane cikin karshen mako, a El Paso da ke jihar Texas da kuma Dayton a jihar Ohio, inda mutane akalla 29 suka halaka, 20 a Texas, 9 kuma a Ohio.

Cikin jawabin nasa Trump ya ce tuni ya baiwa hukumar binciken manyan laifuka ta kasar FBI, umarnin daukar matakai masu tsauri don dakile laifukan kyamar baki, da ayyukan ta’addanci kisan gillar mutanen da ke karuwa cikin kasar ta Amurka.

A baya bayan nan dai shugaban na Amurka ya fuskanci suka mai zafi a ciki da wajen kasar, saboda kalaman da ya furta na nuna wariya ga wasu ‘yan majalisar wakilan kasar mata baki, da kuma matakan da gwamnatinsa ta soma dauka na kame bakin-haure ko yan ci rani marasa rijista don mayar da su kasashen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.