Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka: Obama ya koka kan rashin takaita mallakar bindiga

Tsohon shugaban Amurka Barrack Obama, ya koka bisa yadda gwamnati mai ci a karkashin Donald Trump, ta gaza daukar matakai, na tsaurara dokokin sa ido kan mallakar bindiga tsakanin ‘yan kasar.

Tsohon shugaban Amurka Barrack Obama tare da magoya bayansa a Miami, Amurka.
Tsohon shugaban Amurka Barrack Obama tare da magoya bayansa a Miami, Amurka. Reuters
Talla

Obama ya bayyana haka, ne yayin tsokaci kan halaka mutane akalla 29 da ‘yan bindiga suka yi a Ohio da Dayton a karshen mako, da kuma karuwar matsalar a sassan kasar.

Tsohon shugaban na Amurka y ace abin takaice ne cewar yadda Amurka kasa mafi karfi da ci gaba a duniya, ke fama da matsalar marasa tunani mai saiti, da kuma rashin tsaurara dokokin sa ido wajen mallaka da kuma amfani da bindigogi, duk kuwa da cewar Amurkawa na ci gaba da fuskantar kisan gillar ‘yan bindiga akai akai.

Jawabin na Barrack Obama, martani ne kan kisan gillar da ‘yan bindiga suka yiwa mutane 29 a karshen mako, 20 a El Paso da ke jihar Texas da kuma 9 a Dayton dake jihar Ohio.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.