rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan sanda sun kama masu adawa da gwamnatin Rasha

media
Jami'an 'yan sandan Moscow na murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnati. REUTERS/Maxim Shemetov

Jami’an 'yan sandan kwantar da tarzoma sun kama ‘yan adawa da dama da suka gudanar da gagarumar zanga-zanga a birnin Msocow na Rasha, inda suka bukaci gudanar da sahihin zabe a kasar.


Kimanin ‘yan adawa dubu 50 ne suka fito kan titunan Moscow domin zanga-zangar ta ranar Asabar.

Masu zanga-zangar dauke da alluna sun yi ta wake-waken neman a ba su ‘yancin kada kuri’a, yayinda suka kira shugaban kasar da makaryaci.

Masu zanga-zangar na ci gaba da nuna bacin ransu kan matakin cire sunayen ‘yan adawa daga cikin jerin sunayen ‘yan takarar da za su fafata a zaben kananan hukumomi a cikin watan gobe.

An dai bayyana wannan gangamin a matsayin daya daga cikin zanga-zanga mafi girma da aka gudanar tun bayan komawar shugaba Vladmir Putin kan karagar mulki a shekarar 2012.

A can baya dai, jami’an kwantar da tarzomar sun kama masu irin wannan gangami har dubu 2, lura da cewa sun fantsama kan tituna ne ba tare da izinin mahukunta ba a cewar ‘yan sandan.