Isa ga babban shafi

PSG taki kammala cinikin Neymar

Paris St Germain na kasar Faransa ta ki sallama tayin da takwarorinsa biyu na Spain masu hamayya da juna wato Barcelona da Real Madrid suka yi, na zawarcin dan kwallon tawagar Brazil, dake club din wato Neymar.

Dan wasan gaba na kasar Brazil da PSG wato Neymar.
Dan wasan gaba na kasar Brazil da PSG wato Neymar. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Barcelona ta taya Neymar Jr mai shekaru 27 wanda tsohon dan wasanta ne, fam miliyan 92.4, da kuma hadawa da dan wasanta Philippe Coutinho.

Wasu rahotanni ma sunce cikin tayin na Barcelona harda Karin dan wasanta Ivan Rakitic ga PSG dan ta mallaki Neymar.

Yayin da Kungiyar Real Madrid ta taya Neymar da wasu makudan kudade, kana itama da bayar da 'yan wasanta guda biyu Gareth Bale da kuma James Rodriguez.

Akwai wasu bayanai da ke cewa PSG ta bukaci Madrid ta hada mata da Vinicius Junior, to saidai kungiyar bata bayyana ko ta amince da yin hakan ba.

Dan wasan na Brazil wato Neymar ya zama dan kwallon da ya fi tsada a duniya, lokacin da PSG ta saye shi a shekarar 2017 da zunzurutun kudi har fam miliyan 205, to sai dai yayi ta fama da jinya a club din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.