rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

G7 Faransa Tattalin Arziki Ta'addanci Nukiliya Emmanuel Macron Donald Trump

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa na shirin karban bakwancin taron G7

media
shugaban Faransa Emmanuel Macron da wasu mukarrabansa na shirye-shiryen bakwanci taron kasashen G7 Philippe Lopez/Pool via REUTERS

Gungun kasashen 7 mafiya karfin masana’antu na duniya G7, zasu gudanar da zaman taronsu ranar Assabar zuwa Litanin a Biarritz dake yankin kudu maso Yammacin kasar Faransa.

Kungiyar kasashen da aka kafa a 1975, zai tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziki da makamantansu, kamar tsaro Muhalli da kuma ta’addanci.


A yayin da a ake shirin gudanar da taron a Faransa dake rike da shugabancin karba karbar gungun na kasashen G7, yanzu haka ana fuskantar takun saka tsakanin wasu kasashe mambobin kungiyar da suka hada da manyan kasashe masu karfin masana’antu na duniya, da suka hada Amruka, Canada, Ingila Faransa Italiya, Jamus da kuma Japan

Taron na birnin Biarritz na ranar Assabar zai soma ne cikin tsananin rashin jituwa, tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da sauran kawayensa, dangane da batutuwa da dama, da suka hada da batun aikin samar da makamashin nukliyar Iran, yakin Syiya da kuma yarjejeniyar dumamar yanayi ta birnin paris da dai sauransu..

Har zuwa shekarar da ta gabata dai, duk tarurrukan da Kungiyar ta G7 ke gudanarwa na karewa ne da sanarwar bai daya dake kare muradun kasashen nasu.

Sai dai, a 2018 a kasar Canada, shugaban Amruka Donald Trump yaki saka hannu kan sanarwar bayan taron da shi da kansa ya amince da ita.

A 2017, hadakar kasashen ta gamu da Baraka kan batun dumamar yanayi, kuma shine taron farko da Trump ya halarta a Sicile ba tare da yace uffan ba.

Amma kuma yan kwanaki bayyan taron, ya bayyana fitar da kasarsa daga cikin yarjejeniyar hana dumamar yanayi ta duniya ta birnin Paris.