rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

G7 Faransa Emmanuel Macron Amurka Donald Trump Tattalin Arziki Diflomasiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Manufar Trump kan tattalin arziki barazana ce ga duniya - Macron

media
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron yayin cin abincin rana gabannin soma taron kasashen G7 a Biarritz dake Faransa. 24/8/2019. REUTERS/Carlos Barria

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugaban majalisar kungiyar tarayyar Turai Donald Tusk, sun yi gargadin cewa matakan da shugaban Amurka Donald Trump ke dauka, na haddasa rikicin kasuwanci tsakaninsa da China da kuma sauran kasashen Turai, zai iya jefa tattalin arzikin duniya cikin halin koma baya.


Jagororin biyu sun yi gargadin ne yayinda taron kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki na G7 ya kankama a Faransa.

Tuni dai manyan shugabannin kasashen 7 masu karfin tattalin arziki da masana'antu suka kammala hallara a birnin Biarritz dake kudancin Faransa.

Daga cikin manyan batutuwan da taron kasashen G7 zai maida hankali kai, akwai rikicin kasuwancin Amurka da wasu kasashe, sauyin yanayi da gobarar dajin dake barazanar nakasa dajin Amazon, sai kuma halin da yankin gabas ta tsakiya ke ciki.

Zalika taron zai tattauna kan muhimman batutuwan da suka shafi tsaro da kuma kalubalantar matakin fifita kasa.

Taron dai shi ne irinsa na farko da Fira ministan Birtaniya Boris Johnson zai halarta tun bayan hawansa mulki.