rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia

Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Firaministan Birtaniya ya kulle majalisar kasar gabanin Brexit

media
Firaministan Birtaniya, Boris Johnson Neil Hall/Pool via REUTERS

Firamistan Birtaniya Boris Johnson ya sanar da rufe Majalisar Dokokin kasar har sai ranar 14 ga watan Oktoba, wato makwanni biyu gabanin ficewar kasar daga Kungiyar Tarayyar Turai, lamarin da ya janyo cece- kuce, ya kuma harzuka ‘yan majalisar da ke adawa da ficewar.


Wannan mataki na gwamnatin Birtaniya zai takaita lokacin da ‘yan majalisar masu goyon bayan kungiyar Tarayyar Turai ke da shi a kokarin da su na dankwafe shirin Firaminista Johnson na ficewa daga Tarayyar Turai kafin wa’adin ranar 31 ga watan Oktoba.

Sanarwar ta Johnson na zuwa ne bayan ‘yan majalisar dokoki shida daga jam’iyyar adawa sun bayyana aniyar yin dokar da za ta hana ficewa daga kungiyar Tarayyar Turan ba tare da yarjejeniya ba da zarar majalisar ta dawo hutu a mako mai zuwa.

A halin da ake ciki, Firaministan ya ce ya bai wa Sarauniyar Ingila damar sake bude majalisar tare da gabatar da jawabi a ranar 14 ga watan Oktoba.

‘Yan majalisar dokokin da ke goyon bayan ci gaba da kasancewar Birtaniya a Tarayyar Turai sun mayar da martani cikin fushi, inda suka bayyana Johnson, wanda ya dare mulki cikin watan jiya a matsayin dan kama karya, yayin da kakakin karamar majalisar dokokin kasar John Bercow ya bayyan matakin da cewa baya bisa ka’ida, kuma an dauka ne don yin kafar ungulu ga shirin barin Tarayyar Turai.

A bangare guda shugaba Donald Trump na Amurka ya jinjinawa abin da ya kira ‘jarumtar’ Johnson, yayin da darajar kudin fam na Ingila ta rikito da bayyanar wannan labari da ‘yan adawa ke cewa tamkar ‘juyin mulki’ ne da ayyana yaki.