rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ingila Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kungiyar EFL ta cire sunan kungiyar Bury ta Ingila

media
Wasu daga cikin magoya bayan kungiyar Bury a Ingila Reuters/Ed Sykes

A Ingila hukumar dake sa ido wajen tafiyar da wasannin da suka jibanci kwallon kafa aji yan dagaji EFL ta sanar da janye ko kuma cire sunan kungiyar Bury daga cikin kungiyoyin da ya dace a cigaba da damawa da su a wannan gasa.


Tarihi ya nuna cewa kungiyar ta Bury ta shafe sama da shekara 100 ta na haskawa a duniyar kwallon kafar kasar Ingila tareda lashe kofin Ingila a shekaru na 1900 da 1903, a cewar hukumar ta EFL magabatan Bury sun kasa bulo da hanyoyin ceto kungiyar daga durkushewa.