Isa ga babban shafi
Birtaniya-Tarayyar Turai

Birtaniya na iya barin Turai ba yarjejeniya - EU

Tarayyar Turai ta ce Birtaniya ba ta yi wani tayi mai armashi ba game da sake duba yarjejeiyar ficewar ta daga kungiyar, kuma a halin da ake ciki, kusan tabbas ana iya rabuwa ba tare da an cimma yarjejeniya ba.

Firaministan Birtaniya, Boris Johnson
Firaministan Birtaniya, Boris Johnson Tobias SCHWARZ / AFP
Talla

Wannan bayani daga kungiyar Tarayyar Turai na zuwa ne a daidai lokacin da firaminista Boris Johnson ke yin tsayuwar gwamin jaki a kokarinsa na ficewa da Birtaniya daga kungiyar Turai ko da yarjejeniya ko akasin haka a ranar 31 ga watan Oktoba, ya yin da su kuma ‘yan majalisar Birtaniyan ke kokarin taka mai birki.

Mai magana da yawun hukumar Tarayyar Turai, Mina Andreeva ta ce hukumar ta kaddara cewa Birtaniya za ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai a ranar 31 ga watan Oktoba kuma da haka take aiki, da aka tambayeta ko zata fice babu yarjejeniya, sai ta ce akwai yiwuwar haka ainun.

Firaminista Johnson dai ya dage ko ta halin kaka sai ya jaddada kuri’ar da al’ummar Birtaniya ta kada a zaben raba gardama kan ficewa daga kungiyar Turai a 2016, inda har yayi barazana korar duk wani dan majalisar daga jam’iyyar Conservative mai mulki da ya goyi bayan jinkirta batun ficewa a kuri’ar yau Talata.

Amma barazanar tasa ta yi akasin gyara, saboda da a yau Talata dan majalisa Philip Lee daga jam’iyyar Conservative ya canza sheka zuwa jam’iyyar Liberal Democrats mai adawa da ficewa daga tarayyar Turai,lamarin daya sa yanzu Johnson yab rasa rinjaye a majalisar gabanin kuria’a jinkirta ficewa a 31 ga Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.