Isa ga babban shafi
Turkiya-Turai

Za mu bai wa 'yan gudun hijirar Syria damar shiga Turai-Erdogan

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya yi barazanar bude wa ‘yan gudun hijirar Syria kofa domin kwarara cikin kasashen Turai matukar Kungiyar Tarayyar Turai ta ki bayar da karin tallafi ga kasarsa.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan AFP/Adem Altan
Talla

Turkiya ta kasance gida ga ‘yan gudun hijira miliyan 3 da dubu dari 6, lamarin da ya sa ta yi kira da a samar da tudun-mun-tsira a arewa-maso gabashin Syria da yaki ya daidaita, domin bai wa ‘yan gudun-damar komawa gida.

Shugaba Erdogan wanda ya yi ikirarin cewa kasarsa ta kashe Dala miliyan 40 kan ‘yan gudun hijirar, ya caccaki Kungiyar Kasashen Turai kan rashin cika alkawarinta, yana mai cewa idan har hakan ya ci gaba, zai saki kyaure domin bai wa ‘yan gudun hijirar damar bazuwa cikin kasashen na Turai, saboda kasarsa ba za ta ci gaba da dawainiya da su ita kadai ba a cewarsa.

A karkashin wata yarjejeniya a shekarar 2016, Tarayyar Turai ta yi alkawarin bai wa Turkiya kudaden da suka kai Euro biliyan shida da miliyan dari 6 don ta hana ‘yan gudun hijirar tsallakawa kasashen Turai, amma a cewar Erdogan, biliyan 3 kawai aka samu daga wadannan kudade.

Sai dai Hukumar Tarayyar Turai ta bakin kakakinta, Natasha Bertaud, ta musanta ikirarin na Erdogan, inda ta shaida wa manema labarai a Brussels cewa, ta samar da Euro biliyan biyar da miliyan dari 6 na kudin ga Turkiya, kuma nan ba da jimawa ba za ta cika sauran kudin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.