Isa ga babban shafi
Faransa

Zafi ya kashe mutane dubu 1 da 500 a Faransa

Gwamnatin Faransa ta bayyana cewa, sama da mutane dubu 1 da 500 suka rasa rayukansu sakamakon ibtila’in tsananin zafi da ya afka wa kasar a kwanakin baya.

Tsananin zafin ya tilasta wa mutane zuba ruwa a jikinsu domin samun sa'ida a Faransa
Tsananin zafin ya tilasta wa mutane zuba ruwa a jikinsu domin samun sa'ida a Faransa REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Ministar Lafiyar Faransa, Agnes Buzyn ta ce, sun tattara alkaluman mutane dubu 1 da 500 da suka mutu a cikin watanni biyu, amma ko kusa wadannan alkaluma basu kai wadanda aka samu a shekarar 2003 ba, lokacin da makamancin wannan ibtila’in ya lakume rayuka dubu 15.

Tsananin zafin na shekarar bana, ya afka wa Faransa ne a cikin watannin Yuni da Yuli, inda ya kai digiri 46 a ma’aunin Celsius musamman a yankin kudancin kasar.

A shekarar 2003, tsananin zafin ya addabi jama’a ne cikin kwanaki 20 na watan Agusta, yayinda a bana, ya shafe kwanaki 18 yana hana mutane sukuni a mabanbantan lokuta biyu.

Ministar Lafiyar ta ce, matakan kariyar da hukumomin kasar suka dauka, sun taimaka wajen rage alkaluman mace-macen a bana, idan aka kwatanta da shekarar 2003.

Tarihi ya nuna cewa, shekarar ta 2003, ita ce wadda aka fi samun asarar rayuka sakamakon tsananin zafin a Faransa, inda a wancan lokacin ibtila’in ya fi kamari a birnin Paris da yankin tsakiyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.