rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Matan mujahidan da ke komawa Turai hatsari ne ga nahiyar - rahoto

media
Shugaban majalisar kungiyar kasashen Turai EU, Donald Tusk REUTERS/Christian Hartmann

Wani rahoto kungiyar GLOBSEC ya yi gargadi game da matan mujahidan da ke komawa nahiyar Turai daga kungiyoyin ta’addanci ciki har da IS, yana mai bayyana su a matsayin babbar barazana ga tsaron Nahiyar.


Rahoton kungiyar ta GLOBSEC ya bayyana cewa matan mujahidan maimakon kasancewarsu Amare a hannun mayakan kungiyoyin ta’addancin sun taka muhimmiyar rawa wajen aikata nasu ayyukan ta’addanci ciki har da kaddamar da farmaki wanda kuma ke matsayin barazana ga tsaron kasashen da suka je, ta yiwuwar kaddamar da hare-haren ta’addanci.

Cikin rahoton kungiyar wadda ke da babbar shalkwata a Slovakia ta ce binciken da ta gudanar kan bayanan matan mujahidan 326 da aka kama ko kuma aka kashe tun daga shekarar 2015 zuwa yanzu ya nuna cewa duk da karancinsu za su iya aikata abin da ba a yi tsammani ba ga tsaron kasashen da su ke a yanzu.

A cewar rahoton kungiyar ta GLOBSEC babu shakka mata basu yi karfi wajen iya kaddamar da farmakin ta’addanci ba, amma bayanan sirrin da ta samu kan mata 43 ya nuna cewar suna wakiltar gagarumin shirin harin ta’addanci a Turai.

Haka zalika akwai wasu daga cikin matan 43 da ke cikin wadanda suka yi yunkurin farmakar majami’ar Notre-Dame shekaru 3 da suka gabata.