rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Johnson ya gaza shawo kan EU game da ficewar Birtaniya

media
Firaministan Birtaniya Boris Johnson da shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker REUTERS/Yves Herman

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya gaza wajen shawon kan shugabannin kungiyar Turai cewar yana da wani ngantaccen shirin ficewa daga kungiyar, abinda yasa ya haure takalman sa ya fice ba tare da halartar taron manema labarai ba.


Kafin zuwansa taron, Johnson ya bayyana kan sa a matsayin fitaccen mai shirin fina finai, ‘Icredible Hulk’ wanda ke samun nasara a koda yaushe, amma kuma daga karshe tafiyar tasa ba ta haifar da da mai ido ba.

Firaministan Luxembourg, Xavier Bettel ya shaidawa Johnson cewar ya dace ya daina yawan magana, maimakon haka ya mayar da hankali wajen aiki, bayan da Firaministan na Birtaniya ya fuskanci zanga-zanga mai karfi don nuna adawa da shirin kasar na ficewa daga EU.

Firaminista Bettle wadda da gani ya fusata ainun, ya yi ta nuni da inda tutar Birtaniya take yana kashedin cewa Birtaniya ta kasa bijirowa da wata sahihiyar hanyar farfado da batun ficewarta daga Tarayyar Turai, sannan ya ce lokaci ya yi da ya kamata kasar ta bar cika baki.

Bayan ‘yar gajeruwar tattaunawa da Johnson, Bettle wadda ya nufi birnin Paris don ganawa da shugaba Emmanuela Macron, ya yi kashedin cewa shugabannin Turai ba za su jinkirta batun ficewar Biurtaniya daga Tarayyar Turai ba idan ba ta bijiro da shirinta a rubuce nan ba da jimawa ba.

Johnson wadda ya nace cewa ya samu ci gaba wajen samun karin jerin ganawa da jagoran Tarayyar Turai Jean-Claude Junker da mai shiga tsakani Michel Barnier zai yi jawabi ga majalisar Tarayyar Turai a yau Laraba a birnin Strausbourg, don jaddada aniyarsa ta barin kungiyar.

Kowanne lokaci a yau Laraba ne ake saran ganawar ta gudana tsakanin Firaministan na Birtaniya Boris Johnson da shugaban Faransa Emmanuel Macron.